Taron Da Aka Saba Gudanarwa A Hubbaren Imam Riza A Ranar Farko Ga Muharram
IQNA - An gudanar da wata al'ada ta sawon shekaru mai suna Sala a hubbaren Imam Riza (AS) da ke birnin Mashhad dake arewa maso gabashin kasar Iran a safiyar ranar Lahadin da ta gabata, daya ga watan muharram na hijira.
Sala na nufin kira, sanarwa da gayyata. Bikin wanda ya kunshi kasidu da wakoki mai taken juyayin shahadar Imam Husaini (AS) ana gudanar da shi ne duk shekara sama da karni uku.